DABBOBIN DA AKA HANA CIN NAMAN SU

  ILLOLIN CIN NAMAN DABBOBIN DA AKA HARAMTA A MUSULUNCI


Gabatarwa (Introduction)

Kamar yadda kowa ya sani akwai dabbobin da Ake ci da Kuma wanda Ba'a ci. Wasu daga cikin su Ba'a ci ne saboda Cutarwar su ta fito a sarari. Wasu kuma a boye. Sannan akwai Dabbobin da Musulunci ya hana ci. Wanda daga cikin Dabbobin da Musulunci ya hana ci akwai Jaki, Biri, Kuliya, Alade, Kare.

Abibci yana da Babban Tasiri a rayuwar Ɗan Adam, Wannan kuma ya ta'allaƙa ne akan Haram ne Ko Halal.  

Duk wanda Yake Cin Abinci Na Halal Ko wani Rana, to halayen shi zasu kasance masu kyau, Zuciyar Zata rayuwa, Sannan Zai iya zama silar karban Addu'ar shi, kuma Abincin yayi wa Tinanin shi da jikin shi amfani.

Kenan, Idan Ka Saba da Cin Abinci Na Haram, Halayyar ka zata kasance Mai Muni, Shauƙin shi zai Mutu, Addu'ar shi zatai Wuyar amsuwa, kuma zai rusa jiki da Zuciyar shi. Abune wanda baza'a ƙi yarda ba cewa Abinci yana da Matuƙar daidaita Rayuwar ɗan Adam, Musamman Wajen Girman Shi da Lafiyar jiki.

Halal and Haram Meat


Abubuwan da Zamu Tattauna Sune Illolin Abuncin da Aka Hana Ci:


1. Biri (Monkey)

Cin Naman Biri Yana Da Illa Ga Lafiya. "Jinin Su Da Ƙwayar Halittar Birrai yana Kamanceceniya da Irin Na Ɗan Adam wannan yasa Kamuwa da cutar dabbobi Zai yi sauƙin kama mutum da wuri kamar su Virus da Bacteria Zasu Fito daga Jikin Birrain zuwa jikin Mutum.

Side effect of eating monkey meat


2. Alade (Pig or Pork)

Kamar yadda kowa ya sani Musulunci ya Haramta cin Naman Alade. Haka ma a kimiyance Cin Naman Alade yana Janyo wasu matsaloli Kamar Haka:.

Effect of eating pork

  •  i. Yana Ɗauke da Sinadaran Sodium da Saturated Fats Masu Yawan da Duk wanda ya ci naman Alade zasu iya illata shi.
  • ii. Yana Janyi Cutar Parasite Infection Wacce take saka amai da tashin zuciya, yawan ciwon jiki, ciwon Ciki da yawan Gajiya. Duk waɗannan sukan iya samun Mai cin naman Alade.
  • iii. Yana Kawo Cancer ta Mahaifa Da Sauran Duk Wani Nau'i na Cutar Daji, idan Mutum na Cin Naman Alade yana da Barazanar Kamuwa da Cutar Daji.
  • iv. Yana Sanya Wani Bangare na Jikin Mutum Wato Tissue Mai laushi Ya Koma zuwa Mai Tauri.
  • v. Yana Ɗauke da Wata Guba Wacce take illa ga Lafiyar ɗan Adam.
  • vi. Yana Saka Barazanar Kamuwa da Stroke wanda ke toshe magudanan Jini.



3. Naman Jaki (Donkey)

Naman Jaki Yana Da Cutarwa Ga Lafiyar Ɗan Adam domin yana janyo "cardiovascular diseases" shine Wanna  Cutar Tana Saka Ciwon zuciya da Toshe Magudanan jini, Sai "inflammatory problems" Wato Kumburi Kaga Mutum shikaɗai Yana Kumbura a Rasa Meke damun shi, Sai Kuna "chronic diseases" Cututtuka Wanda Basa Warkewa da Wuri.

Effect of eating donkey meat

Duk wanda ke cin Naman Jaki Yana cikin Barazanar Kamuwa da Irin Waɗannan Cututtuka.

4. Mushe 

Kada Kuyi mamaki Domin akwai mutanen da suke cin mushe a wannar duniyar tamun. Shidai illan cin mushe shine Baka San Me ya Kashe Wannan Abun ba kuma ka ɗauka kaci to Idan cutace ta kashe abun kaima zaka iya kamuwa dashi kuma har takai ga kaima ka mutu ko tayi maka babban illa.

5. Jini

Duk Wata Cuta Idan Zata Shiga Jikin Abu Mai Rai Ko Mai Jini To Tana Kwanciya ne a cikin Jini Wannan Dalilin Yasa Duk wanda yake shan Jini zaka ga baida Isheshshen lafiya kuma rayuwar shi na cikin Barazana na kamuwa da Ko wace irin cuta.


6. Bera da Maciji

Cin Naman Bera ko Maciji Ko cin Abuncin da Aka Saka Naman bera kona Maciji, Ko Cin Abuncin da Bera ta Taba, Yana Kawo Cutar "Salmonellosis" wata Ƙwayar Cutace da take kama jiki Mutum wacce alamomin Ta Sun Haɗa da Gudawa, Zazzabi da Ciwon Ciki kuma yana Iya Kaiwa Kwana Huɗu ko 7 kafun ya Nuna Ko ya Daina.

Karanta: 

7. Kare (Dog Meat)

Cin Naman Kare Yana Da Matuƙar hatsari ga Lafiyar wanda yaci domin yana kawo ciwon Hauka wanda kowa yasan idan kare ya ciji mutun yana iya mutuwa ma idan Ba'a yi masa magani akan lokaci ba ko ma mutum ya haukace.

Effect of eating Dog meat

Ta Iya Yiyuwa Wasu suce ai suna ganin wasu na cin naman kare amma babu abunda ya samesu, to wasu Cututtukan Basa nunawa nan take sai sun ɗau Lokaci mai tsawo wasu ma basa Nunawa akan wanda yaci sai akan ɗan sa ko jikan shi domin akwai cuta mai bin dangi.


Rufewa (Conclusion)

Kamar Yadda Muka Karanta Cututtuka da suke haifar wato Waɗannan Namun Dajin Hanya mai sauƙi da Za'a iya gujewa da kamuwa da Su Shine kawai a Kiyaye Cin naman su. Duk inda kaje Kana Baƙo kuma za kaci nama to kayi Tambaya Saboda Lafiyar jikin ka.


Domin Tabbatar da Ingancin Rubutun mu Zaku iya Yin Bincike.

Post a Comment

Previous Post Next Post