YADDA AKE SACE ZUCIYAR NAMIJI

YADDA AKE SOYAYYA DA SACE ZUCIYAR SAURAYI

Soyayya wani abu ne mai matukar kyau da ke cike da jin dadin zuciya, amma kuma tana da kalubale da dama. Sace zuciyar saurayi ba kawai yana nufin samun sha'awa daga gare shi ba, har ma yana nufin gina dangantaka mai karfi da juna. A cikin wannan rubutun, za mu tattauna hanyoyi da dabaru da za su taimaka wajen sace zuciyar saurayi da kuma gina soyayya mai dorewa.

1. Fahimtar Juna

Fahimtar juna na daga cikin muhimman abubuwa a kowanne irin dangantaka. Ka fara da sanin abin da saurayinka yake so da kuma abubuwan da ba ya so. Wannan yana nufin yin nazari kan halayensa, abubuwan da yake sha'awa, da kuma abubuwan da suka shafe shi a rayuwarsa. Idan ka san abin da yake so, za ka iya tsara abubuwa da zasu faranta masa rai.

2. Kirkirar Lokaci Mai Kyau

Daya daga cikin hanyoyin da zaka iya sace zuciyar saurayi shine ta hanyar kirkirar lokuta masu kyau tare. Yi kokarin shirya abubuwan da zasu kasance na musamman, kamar fita zuwa wurare masu kyau, ko kuma yin abubuwan da kuke so tare. Wannan zai ba ku damar jin dadin juna da kuma kara kusanci. Hakanan zaka iya tunanin shirya wani taron da zai ba ku damar jin dadin juna a cikin yanayi mai kyau.




Domin Sayan Data Mai Sauki a Ziyarci https://www.elsub.com.ng 


3. Tattaunawa da Jin Ra'ayi

Tattaunawa mai kyau na da matukar muhimmanci a cikin dangantaka. Ka yi kokarin tattaunawa da saurayinka akan abubuwa da dama, daga abubuwan da suka faru a yau da kullum har zuwa ra'ayoyi masu zurfi. Ka kasance mai sauraro sosai, ka nuna masa cewa kana da sha'awar ra'ayinsa da tunaninsa. Wannan zai sa ya ji cewa yana da muhimmanci a gare ka.

4. Girmama Ra'ayinsa

Girmama ra'ayinsa da zabi na daga cikin hanyoyin da za su sa ya ji dadin kasancewa tare da kai. Ko da kuwa kuna da bambancin ra'ayi a wasu lokuta, yana da kyau ka nuna masa cewa kana girmama ra'ayinsa. Wannan zai sa ya ji cewa kana da hakuri da kuma juriya a cikin dangantakarku.

5. Kyaututtuka da Hadi

Kyaututtuka na iya zama hanya mai kyau ta nuna masa cewa kana kula da shi. Wannan ba yana nufin cewa dole ne ka sayi masa abubuwa masu tsada ba, amma yana iya zama kyautar da ta dace da bukatunsa ko sha'awarsa. Misali, idan yana son wani shahararren littafi, zaka iya yi masa kyauta a matsayin tunawa. Wannan zai sa ya ji cewa kana tunani akansa.

Karanta: YADDA-AKE-HIRA-DA-BAZAWARA

6. Aminci da Gaskiya

Aminci da gaskiya su ne ginshikan kowanne irin dangantaka. Ka nuna masa cewa kana da gaskiya da amana a cikin soyayyarku. Kada ka yi masa karya ko kuma ka boye masa wani abu mai mahimmanci. Wannan zai sa ya ji cewa yana da damar dogaro da kai, wanda zai kara karfafa dangantakarku.

7. Taimako da Goyon Baya

Ka kasance a shirye don taimaka masa a lokacin da yake bukata. Ko yana cikin damuwa ko kuma yana fuskantar kalubale, kasancewa tare da shi da bayar da goyon baya zai sa ya ji cewa kana tare da shi a kowane lokaci. Hakan na iya zama ta hanyar bayar da shawara ko kuma kawai kasancewa tare da shi a lokacin da yake bukata.

8. Neman Hangen Nesa

Ka kasance mai hankali da jin dadin sa. Ka fahimci abin da yake so da abubuwan da suka shafe shi. Wannan yana nufin ka yi nazari kan halayensa da abubuwan da ke faranta masa rai. Idan ka san abin da yake so, zaka iya tsara abubuwa da zasu jawo hankalinsa.

9. Kula da Kanka

Kula da kanka na da matukar muhimmanci a cikin dangantaka. Ka kasance mai kyau a wajen kanka, ka kula da lafiyarka da kuma jin dadin ka. Idan ka kasance cikin koshin lafiya da jin dadi, hakan zai sa ka fi jin dadin kasancewa tare da saurayinka. Hakanan yana da kyau ka kasance mai jituwa da kanka, domin hakan na iya zama abin jan hankali ga saurayin.

10. Kasancewa Mai Kyau

Kasancewa mai kyau yana da matukar muhimmanci a cikin dangantaka. Ka kasance mai kyau a wajen jiki da tunani. Wannan ba yana nufin cewa dole ne ka zama mutum mai kyau ba, amma yana nufin ka kasance mai kyawawan halaye da dabi'u. Kasancewa mai kyau yana jawo hankalin mutane da dama, ciki har da saurayin ka.

Daga Ƙarshe

Sace zuciyar saurayi ba abu ne mai sauki ba, amma tare da hakuri da juriya, zaku iya samun nasara. Ka tuna cewa soyayya tana bukatar lokaci da kokari. Yi amfani da shawarwarin da aka bayar a sama, ka gina dangantaka mai karfi da juna. Kada ka manta, a karshe, soyayya tana da matukar daraja, kuma yana da kyau ka yi kokari don ganin ta girma a cikin zuciyar ku.


 YADDA ZAKI MALLAKE SAURAYIN KI

Dayawa yan matan arewa ko nace ƙasar hausa suna da wani naƙasu a soyayya hakan yasa sauran ƙabilu sukafisu cin ribar soyayya misamman waje iya mallakar namiji.

Abun Mamaki Sai Kaga Wacce Take Yin Yare, Gata Mummuna Amma Saurayinta Duk duniya Ba Wacce Yakeso Sai Ita Saboda Yadda Yake Marari Akanta Da Sonta. Sakamakon Kulawa Da Take Bashi A Soyayya Da Ƙwarewa Wajen Iya Kalamai Da Tsari Na Soyayya,



In kunyi nazari dayawa yan matan qabilu kamar yoruba igbo, indiya, china, tu­rawa ,su a soyayya kullun burin su daÉ—aÉ—awa masoyin su suke da son suburgeshi son ya gani ya yaba, da kuma jan hankalin sa. hakan yasa suke gane meson su nahaqiqa bana sha'awa ba, sai kaga suna soyayyar su cikin kwanciyar hankali, da taimakon juna kamar wa da Æ™anwa.


sabanin mu nan yan matan mu, dazarar kafara soyayya to watan baƙinciki yakama a rayuwar ka, kataro mach babba haka zaka kasance cikin damuwa yau dadi gobe baqin ciki. wai kullin kai sai dai ka rarrasheta, saidai kafaranta mata rai.


Advertisement: Buy Data Subscription at Very Chip Price  Visit:

https://www.elsub.com.ng 




1. Idan ka ƙira a waya bazata ɗauka da wuri ba.
2. Idan kaje zance taita wani nuƙu-nuƙu kan ta fito.



3. Idan tabuƙaci wani abu baka bata ba taita fushi dakai sai kace ta baka ajiya.
4. Kuyi ta faÉ—a akan akwati da lefe ,tana sai kayi 12 kana 6, ko kana 3 zakai tana cewa sai kayi 4, ba tausayi yadda kasan ATM Card haka suka maida namiji mafiya yawan Æ´an matan hausa haka suke.

Babu abunda yafi cutar da yan matan arewa a soyayya irin RASHIN NUNA SOYAYYA GA MASOYI wai namiji akwai wulaÆ™anci dan haka sai anjamasa aji over. 
Bata san duk namijin da yazo wurin ki domin aure baya son jan aji ba.




AMATSAYIN KI NA BUDURWA GA YADDA ZAKI MALLAKE SAURAYINKI.

1. tashin farko kizama me kyakkyawan hali kamar gaskiya, HaÆ™uri, barin zargi, riÆ™on amana  KAMUN KAI, kunya da sauran su.




2. kizama me murmushi ga masoyinki ba me hade rai ba, ba kuma koda yaushe ba kamar kina tallan makilin.

Shi murmushi anayin sa ne yayin gai da masoyi, ko ban kwana da masoyi, ko yayin da akai wa juna satar kallo, ko yayin da aka hadu a hanya ko farkon hira, ko yayin da masoyi yafadi magana me daÉ—i.




YADDA ZAKIYI MURMUSHI
kidan tabe kumatunki tare da bude bakinki kamar kaso 1 cikin goma tayadda haƙoran sama yawanci masu faffadan haƙora yayin murmushi haƙora 6 ko 7 na gaba ne suke bayyana, amma masu qananan haƙora sukan zarta hakan sannan gefen dadashin sama ma in yafito kadan abun yafi armashi, sannan ana so ki dan karkatara da kanki, ko ki motsashi ko kiyi qasa da kanki kadan, yayin murmushi ana hadashi DA kallon qauna wato irin kallon da kwayar ido take komawa 55 angle na ido, ko wanda ake maida ƙwayan ido gefe irin na kallon kahadu fa.


Yar uwa murmushi nasa ki mallake saurayi sosai. SANNAN AKWAI MURMUSHI NA GANIN dama

3. nuna soyayya ga saurayinki, wato ta wadannan han yoyin
- Mai dama sa da Saƙo (Text) in yayi miki, wato reply na Saƙo domin wasu saidai kaita aikamusu saqon amma susai sun gadama zasu dawo ma dashi.


Wata sai ka taƙarƙare kayi mata kalamai masu yawa amma intatashi yimasa reply saikaga kolayi daya baikaiaba kamar bata so misali kaji tace .
- nagode nawan, ko kai nawan, ko gaskiya naji dadi, ko hmm nagode da sauran su. duk wannan ba daidai bane, yakamata yadda ya bata lokaci kema ki ƙoƙarta ki yi koda layi 3 kema ki aikamasa tabbas zai ji dadi.

- Kiran sa a lokacin da bai zataba musamman a lokacin da kike zaton yana cikin abokan sa, ko yana nishadi, a duk sadda kika kira shi yaÉ—au wayan sa yaga sunanki murmushi yakan farayi koda yana cikin abokan sa zai tashi da sauri in an tambayeshi me ya faru zai ce mutuniyarce yana murmushi. hakan yakan ji dadi kin kuma burgeshi kin kira shi a cikin abokansa dansusan kin damu da shi. Kuma ko zasu zugashi akan ki zasu bashi shawari ne me kyau.-

Amma da yawan Æ´an mata, su sai dai kaita kiransu wata inkaga takiraka to tana buqatar wani abune ko kayi mata gorin kira, wata sai jarabar flashing kamar Jikar MTN.


- Yi masa kyauta, ta bazata komai ƙanƙantarsa musali saya masa zobe, turamasa kati koda na 10 wlh inyasan arzikin ki daidai hakan ne zai ji dadi sosai, yasan yana ranki, ko ɗan mintin nan na 30 kacal.

- Furta masa kalaman soyayya koda rabin yadda shi yake furta miki ne .

- kula da lukutan sa na zuwa Hira, neman afuwar sa in kin saba lokaci, nuna masa damuwarki in yasaba lokaci ko bai zoba har sai ya rarrasheki.

- Yawaita yimasa nasiha cikin wasa da shagwaba

- yin kwalliya yayin zuwan sa Hira, dakuma nuna masa damuwa in bai yaba kwalliyar ba.

- Nuna tausayin sa dakuma tayashi farin ciki ayayin da farinciki ya sameshi dakuma tayashi bacin rai ayayin da baƙin ciki yasameshi, da ƙoƙarin kwantar mashi da hankali.


- Girmama iyayensa .
- Nuna nishaÉ—i da jindadi yayin daya zo gunki.
- Kada ki tsawaita jan aji a gareshi, idan kika dan ja kadan, to zai rarrasheki, daga nan kekuma sai ki haqura,

- Kina nuna masa kina da matsayi da kima da aji ba kowani namiji yadace dake ba sai shi.

- kizama me tsari da kama mutuncinki da sanin Æ´ancinki a soyayya misali: ki nuna masa bacin ranki in zai saki sabon Allah koda zai dena zuwa dakan sa zai nemi gafarar ki.

- kada kizama me izza ga saurayi da nuna wa samari ke ba wani namiji da ya isa kiyi masa kaza da kaza SAMARI SUN TSANI HAKA! 

- Ki Zama Me Fuska Daya.
- Kada Kisa Girman Kai Ga Saurayin Ki,
- Kada Kuma Ki Nuna Masa Ke Marar Ƴanci Ce. Kamar In Baki Same Shi ba Mutuwa Za Kiyi A'a, Kidai Nuna Masa So Dai Dai Misali. Kada Ki boye Qaunar Da Kike Masa

Advertisement: Buy Data Subscription at Very Chip Price  Visit:

https://www.elsub.com.ng 

Post a Comment

Previous Post Next Post